Isa ga babban shafi
INDIA

India ta bullo da inshora don hana manoma kashe kansu saboda rashin samun anfanin gona

Gwamnatin kasar India, ta bullo da wani shirin inshora domin taimakawa manomar kasar, sakamakon yadda wasu manoma ke kashe kansu saboda fari da kasar ke fuskanta a shekaru biyu da suka gabata.

karancin ruwan sama a gonaki
karancin ruwan sama a gonaki សហការី
Talla

Gwamnatin ta Indiya ta ware dalar Amurka Bilyan daya da milyan 300, domin ragewa manoman radadin irin asarar da suka yi a cikin shekarun biyu, wanda sakamakon haka wasu daga cikin manoman suka fara kashe kansu saboda rashin samun amfanin gona a lokacin girbi.

Ministan cikin gidan kasar Rajnath Singh, ya ce a karkashin wannan manomi zai biya kashi daya da digo daya cikin dari na amfanin gonar da yake tunanin cewa zai girbe a karshen kaka, to amma idan aka samu asara sakamakon fari, inshora za ta biya su kashi dari cikin dari na amfanin gonar.

Wasu dai na ganin cewa aiwatar da wannan shiri zai taimaka wa firaminista Nerendra Modi, domin kara samun farin jini a tsakanin al’ummar musamman mazauna yankunan karkara da mafi yawansu manoma ne.

Za a fara aiwatar da shirin ne dai a farkon watan afrilu mai zuwa, kuma a matakin farko zai shafi akalla kashi 23 cikin dari na manoman kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.