Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan na bikin tunawa da mutuwar dalibai

Yau ne kasar Pakistan ke bikin tunawa da mutane 151 da kungiyar Taliban ta hallaka a kazamin harin da ta kai a makarantar sojoji da ke birnin Peshawar a bara, lamarin da ya girgiza kasar wadda ta shafe tsawon shekaru tana fama da hare hare.

Hutunan dalibai da malaman makarantar da Taliban ta kashe a bara.
Hutunan dalibai da malaman makarantar da Taliban ta kashe a bara.
Talla

A karon farko kenan da aka gudanar da irin wannan bikin na tunawa dalibai da malamai da harin ya ritsa da su kuma mayakan Taliban 9 ne suka kaddamar da harin wanda aka bayyana a matsayin mafi muni da kasar tav fuskanta.

Bikin wanda aka gudanar a makarantar gwamnati ta sojoji ya samu halartar firaministan Pakistan, Nawaz Sharif da kuma shugaban ‘yan adawar kasar Imran Khan, har ma da shugaban sojin kasar, Raheel Sharif wanda ya mika gaisuwa ta musamman ga iyayen yara 134 da suka rasa rayukansu a harin.

Gabanin bude taron dai, iyayen yaran sun ziyarci kaburruran ‘ya‘yansu da ke birnin Peshawar yayin da gwamnati ta girke jami’an tsaro a manyan biranen kasar domin tabbatar da tsaro saboda bikin na yau, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa, AFP.

Wani dalibi mai shekaru 13 ya shaida wa AFP cewa, kungiyar Taliban na bukatar dakatar da su daga ci gaba da karatunsu amma hakan ba za ta yiwu ba, sannan ya ce, ilimi shi ne babban makamin da za su yi amfani da shi domin rama abinda Taliban ta yi musu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.