Isa ga babban shafi
China

‘Yar Madigo ta maka gwamnatin China Kotu

Wata ‘Yar Madigo a China ta shigar da kara a kotu domin kalubalantar gwamnatin kasar kan wasu littattafai da aka rubuta da ke bayyanasu a matsayin masu tabin hankali.

Auren Madigo a Taiwan
Auren Madigo a Taiwan Reuters
Talla

A shekara ta 1997 China ta cire luwadi da madigo daga cikin ayyukan laifi, tare da cire su daga cikin jerin sunayen ire-iren tabin hankali.

Wata daliba mai suna Qui Bai a Jami’ar Yat-sen da ke Guangzhou ta bukaci ma’aikatar ilimi a China ta yi bayani akan yadda ma’aikatar ke amincewa da litattafan da aka rubuta da kuma yadda za a sauya su.

Wata kungiyar kare hakkin ‘Yan Madigo tace Litattafai 90 da aka aje a dakin Karatu a Jami’ar Guangzhou sun danganta Luwadi da Madigo a matsayin wata cuta ko tabin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.