Isa ga babban shafi
Bangladesh

Bangladesh ta haramta amfani da Facebook saboda Tsaro

Hukumomin kasar Bangladesh sun sanar da dokar hana amfani da duk hanyoyin sadarwa kamar su facebook ko watsapp dama duk wata hanyar aika sako na wani lokaci har sai an tabbatar babu barazanar tsaro ga zaman lafiyar kasar.

Shugaban kasar Bangladesh Abdul Hamid katika
Shugaban kasar Bangladesh Abdul Hamid katika AFP/AFP/Archives
Talla

Wannan mataki na tsaro da hukumomin kasar Bangladesh suka karfafa ya biyo bayan fargabar barkewar rikici bayan hukuncin kisa da kotu ta zartas a kan wasu ‘yan gwagwarmayar kasar biyu da aka samu da laifin aikata laifufukan yaki.

A yau talata Gwamnatin kasar ta sake matsa kaimi wajen ganin babu wani mahaluki da ke da yancin yin anfani da duk wata hanyar sadarwa wajen aika sako har sai an rataya mutanen biyu.

Su kuma a nasu bangaren kamfanonin sadarwa sun nuna rashin gamsuwa da dokar inda suka bukaci al’ummar kasar da su fito su yi zanga-zanga.

Hukumomi a kasar Bangladesh, sun zartas da hukuncin kisa akan Ali Ahsan Mohammad Mujahid da kuma Salahuddin Quader Chowdury a ranar lahadi da ta gabata bayan samun su da aikata miyagun laifufuka a lokacin da kasar ke gwagwarmayar ballewa daga Pakistan a shekarun 1970.

Kasar Bangladesh ta dau wannan matakin tsaro na rufe hanyar sadarwa, ganin a shekara ta 2013 hukunci makamancin hakan ya haifar da mumunar rikici inda mutane sama da 500 suka rasa rayukansu a arangama tsakanin masu zanga zangar da ‘yansanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.