Isa ga babban shafi
Faransa-China

An cimma yarjejeniyar Nukliya tsakanin Areva da CNNC na China

Katafaren kamfanin samar da makamashin Nukliya na kasar Fransa Areva, a yau litanin a birnin Pekin na kasar China ya bayyana saka hannu kan wata yarjejeniyar aiki da takwaransa na kasar China CNNC.

Ginin kamfanin samar da Nukliya na kasar Fransa Areva
Ginin kamfanin samar da Nukliya na kasar Fransa Areva Reuters/路透社
Talla

Yarjejeniyar da ka sakawa hannu albarkacin ziyarar aikin da shugaban kasar Fransa François Hollande ya kai a kasar Chana, ta bukaci karfafa huldar masana’antu tsakanin Areva da kamfanin nukliyar kasar China CNNC, dangane da ayukan da suka shafi Uranium : hako shi, tace shi, samar da kayyakin aiki, gine-gine da dai makamantansu, kamar yadda kamfanin na Areva ya sanar a yau litanin.

Wannan yarjejeniya dai bata shafi maganar kokarin da ake na sallada kula da ayukan injinan nukliyar samar da makamashi na Areva ga kamfanin samar da makamashin wutar lantarkin kasar Fransa EDF ba.

Sabuwar hulda da ke tattare da amfanin mai yawan gaske, ga kamfanonin 2 Areva da takwaransa na Chana CNNC.

A lokacin da ake gudanar da shagulgulan saka hannu a kan yarjejeniyar a yau litanin a birnin Pékin ko Beijing, Shugaban komitin zartarwar kamfanin Areva Philippe Varin, ya ce kara fadada huldar da suka yi, da abukan huldarsu na kasar Chana, wani babban ci gaba ne ga kamfanin Areva nan gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.