Isa ga babban shafi
Nepal

Jam'iyar Kominisanci ta kafa gwamnati a Nepal

A yau lahadi ne aka zabi shugaban jami’iyar kwaminisanci a kasar Nepal wato KP Sharma Oli a matsayin sabon Firaminista a kasar da girgizar kasar da ta wakana a cikin watan Afrilun wannan shekara ta daidaita, da kuma ta fara aiki da sabon kundin tsarin mulkinta.

shugaban jami'iyar Kominisanci a kasar Nepal Khadga Prashad Sharma Oli ya zama Frayi Minista
shugaban jami'iyar Kominisanci a kasar Nepal Khadga Prashad Sharma Oli ya zama Frayi Minista REUTERS/Navesh Chitrakar
Talla

Shugaban jam’iyar mai tsatsauran ra’ayi ya samu kuri’u 338 a kan 249 da tsohon firaministan mai barin gado Sushil Koirala, wanda a ranar asabar da ta gabata ya yi murabus daga kan mukaminsa bayan da sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka amince da shi a ranar 24 ga watan satumba ya bukaci yin haka

Sabon Firaminista KP Sharma Oli, dan shekaru 63 a duniya na da nauyin sake gina kasar ta Nepal bayan da mummunar girgizar kasar da ta yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane dubu 8,900 a cikin watan Afrilun da ya gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.