Isa ga babban shafi
IRAKI

Iraki ta kai hari kan ayarin motocin shugaban ISIS

Dakarun Sojan kasar Iraki sun bayyana cewa wani hari ta jiragen sama da suka kai a yau ya shafi ayarin motocin shugaban kungiyar ISIS Abu Bakr al Bagdadi, daya daga cikin mutanen da aka fi nema ruwa jallo a duniya , sai dai rundunar ta Iraki ta ce bata da wani karin haske a halin yanzu dangane da makomar shugaban na ISIS yana raye ko a mace.

shugaban kungiyar mujhidan Isis  Abou Bakr al-Bagdhadi à Mossoul,
shugaban kungiyar mujhidan Isis Abou Bakr al-Bagdhadi à Mossoul, AFP PHOTO / HO / AL-FURQAN MEDIA
Talla

A kasar Syria mai makwabtaka da Iraki kuma, inda kungiyar ta ISI ke ci gaba da shan kashi a wajen dakarun gwamnatin Bashar Al’assad da ke samun tallafin jiragen saman kasar Rasha da kuma mayakan sa - kai ta kasar sun kwace wasu filaye daga hannu ‘yan tawayen kasar da ke samun tallafi daga kasahen yammacin duniya dake bukatar ganin bayan gwamnatin shugaba Bashar al Assad.

Kasar ta Iraki dai ta bayyana kai harin akan ayarin motocin shugaban kungiyar ta ISIS dake dauke da dubban dakaru wadanda ke da alhakin keta rigar mutuncin dan adam a duniya.
Yanzu haka dai kungiyar ta ISIS tana rike da kusan kashi 50 cikin 100 na fadin kasar Siriya da kuma wani babban yanki a kasar Iraki.

Yau da sama da shekara guda ke nan hadin guiwar rundunar hadakar kasashen duniya karkashin jagorancin kasar Amruka ke kai hare harenta a kan mayakan na kungiyar a yayinda a ranar 30 ga watan Satumbar da ya gabata kasar Rasha ta shigo inda ta zafafa hare haren babu kakkautawa a kan mayakan na ISIS da ‘yan tawayen kasar Siriya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.