An kashe dan Jaridar Anatolia a Syria
Wani dan jarida mai daukar hoto dake yi wa kamfanin dillancin labaran Anatolia na kasar Turkiya aiki a kasar Syria, ya rasa ransa a cikin wani harin kunar bakin wake da aka kai a yankin Aleppo dake arewacin kasar ta Syria.
Wallafawa ranar:
Saleh Mahmoud Laila mai shekaru 27 ya rasa ransa ne tare da wasu mutane akalla 19 a harin wanda aka kai a kasuwar garin Hraytan dake yankin Aleppo, inda ake tafka kazamin fada tsakanin mayakan Jihadi na ISIS da ‘yan tawaye masu adawa da su.
A watan yulin da ya gabata ne Laila ya tsira daga hare haren jiragen sama da dakarun shugaba Bashar al-Assad su ka kaddamar, yayin da ya yi fama da jinya sakamakon raunukan da ya samu a hare haren, inda aka kwantar da shi a wani asibiti da ke Turkiya.
Tuni dai shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana bacin ransa kan mutuwar dan jaridar tare da mika sakon ta’aziya ga iyalansa da kuma kamfanin dillacin labaran na Anatolia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu