Isa ga babban shafi
Yemen

Firaministan Yemen ya tsallake rijiya da baya a Aden

Firaministan kasar Yemen Khaled Bahah ya tsallake Rijiya da baya, daga wani harin roka da aka kai a kan hotel din da yake ciki a yau talata a birnin Aden da ke kudancin kasar, kamar yadda wani mamba a gwamnatin kasar ya sanar.

Firaministan Yemen Khaled Bahah
Firaministan Yemen Khaled Bahah REUTERS/Khaled Abdullah/Files
Talla

Ministan matasa da wasannin motsa jikin kasar Nayef al-Bakri, ya ce Khaled Bahah na cikin koshin lafiya kuma babu abinda ya same shi.

A yayin da wasu majiyoyin tsaro da shaidun gani da Ido ke cewa, kawo lokacin rubuta wannan labari wuta na ci gaba da cin Hotel din, da aka kaiwa harin rokoki guda 2.

Wata majiyar mahukuntan yankin da bata bayyana sunanta ba, ta ce an samu asarar rayuka da jikkatar mutane da dama a harin.

Yanzu motocin daukar marasa lafiya na kai kawo wajen kwashe gawarwaki wadan da suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.