Isa ga babban shafi
Amurka-Iraqi

Iraqi ta fara amfani da jiragen saman yakin da ta sayo daga Amurka

Gwamnatin kasar Iraqi ta fara amfani da wasu jiragen yaki na musamman, da ta samo daga Amurka domin fafatawa da kungiyar IS nasu daawar jihadi a yankin gabas ta tsakiya.

wasu jiragen saman yaki
wasu jiragen saman yaki REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Kwamandan sojan sama na kasar Staff Laftana Anwar Hama Amin ya shaidawa kamfanin Dillancin labarun Faransa na AFP cewa cikin kwanaki 4 da suka gabata anyi amfani da wadannan jiragen yaki guda 15, domin tarwatsa sansanonin masu ‘yan ta’addan.

Yace an kai harin ne da jiragen sama samfurin F-16 a yankin Salaheddin da kuma Kirkuk.
Cikin watan Yuli zangon farko na jiragen 4 suka isa kasar ta Iraqi, cikin 36 da mahukuntan birnin washigton suka mince su sayarwa mahukuntan birnin Baghdad.
A baya an yita musayar yawu kan cinikin, bayan da Iran ta koka kan yadda Amurka ke jan kafa wajen mika mata jiragen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.