Isa ga babban shafi
Syria-Iraq

ISIL na ci gaba da yin lahani a wuraren tarihi

Mayakan ISIL sun lalata wurin ibadar Baal Shamin da ke Palmyra na kasar Syria, a ci gaba da ruguza dadadun kayayyakin tarihi da suke yi a gabas ta tsakiya.Tun a lokacin da mayakan suka kaddamar da kafa daular Musulunci a Iraqi da Syria suke bibiyan kayayakin tarihi da ake alfahari da su shekaru aru-aru.

Palmyra
Palmyra REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

A cewar shugaban adana kayayakin tarihi na kasar Syria Mamoun Abdulhakim mayakan kungiyar ISIL sun lalata wurin da abubuwa masu fashewa ne.

Ko a kwana bayan mayakan sun kaddamar da wani gangami a Iraqi inda suka lalata tare da sace adananun kayayakin tarihi su siyar.

A wani fai-fai vidiyo da Mayakan na ISIL suka fitar a watan Fabairu su nuna yadda suke amfani da karfi wajen tarwatsa gine-gine tarihi a Birinin Mosul, lamarin da ya mutuka jan hankalin duniya.

Hukumar adana kayayakin tarihi kasar ta ce akalla kayayakin tarihi 90 mayakan sukayi wa illa, wanda suka hada da litatafai da wasiku.

Haka zalika a bara mayakan sun ziyarci wajen bauta Nabi Yunus da ke arewacin kasar inda Musulmi da Krista ke kai ziyarar mai dauke da tarihi tun kafin zuwan annabi Isa AS suka tafka ta'adi.

Ko a kasar Libya Mayakan ISIL sun lalata abubuwa da dama da suka hadda da Hubbare bayan bayyana shi a matsayin abin da ya sabawa addini.

Kazalika a Mali da Afgahinitan inda su kuma al-qaeda da Taliban ke nasu ta’adin da abubuwan tarihin kaka da kakani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.