Isa ga babban shafi
Afghanistan-NATO

Wani hari ta'addanci ya kashe mutane 10 da suka hada da dakaru Nato 3 a Afghanistan

Wani harin kunar bakin waken da aka kai a yau assabar a birnin Kabul na kasar Afghanistan, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10 kamar yadda hukumomin kiyon lafiyar kasar suka sanar

yan sanda a Kabul inda aka kai harin ta'addanci
yan sanda a Kabul inda aka kai harin ta'addanci REUTERS/Ahmad Masood
Talla

Harin da kawo yanzu babu wanda ya dauki nauyin kai shi yayi sanadiyar mutuwar wasu mutane uku ma’aikatan rundunar tsaro ta Nato a Afghanistan.

Bisa dukkanin alamu dai, ana ganin harin baya wuce aikin kungiya Taliban dake ci gaba da haifar da zaman zullumi a kasar, tun bayan kifar da gwamnatinta da Amruka tare da kawayenta na rundunar tsaro ta NATO suka yi a 2001
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.