Isa ga babban shafi
Sri Lanka

An rantsar da Wickremesinghe a Sri Lanka

An rantsar da Ranil Wickremesinghe a matsayin Firaministan kasar Sri Lanka a yau Juma’a bayan ya samu goyon bayan babbar Jam’iyyar adawa domin kafa gwamnatin hadaka.

Ranil Wickremesinghe na karbar rantsuwar shugabanci a matsayin Firaministan Sri Lanka
Ranil Wickremesinghe na karbar rantsuwar shugabanci a matsayin Firaministan Sri Lanka REUTERS/Dinuka Liyanawatte
Talla

Jam’iyyar Sri Lanka Freedom Party ta tsohon shugaban kasa Mahinda Rajapakse mai adawa ta amince ta kulla kawance da Jam’iyyar UNP ta Wickremesinghe.

Sai dai babu bayani akan yarjejeniyar da jam’iyyun biyu suka kulla domin kafa gwamnatin hadin kai a tsakaninsu.

Ana sa ran jam’iyyar SLFP za ta samu mukamai ministoci a sabuwar gwamnatin da za a kafa ta Wickremesinghe.

Jam’iyyar Wickremesinghe ta UNP dai ta samu rinjayen kujeru a a zauren majalisar Sri Lanka mai kujeru 225 a zaben da aka gudanar a ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.