Isa ga babban shafi
Iraqi

An yi zanga zangar adawa da cin hanci a Iraki

Dubban jama’a sun gudanar da zanga zanga a birnin Baghdad na Kasar Iraki domin nuna rashin amincewarsu kan matsalar cin hanci da rashawa da kasar ke fama da ita.

Firai Ministan Iraki, Haidar Al-Abadi
Firai Ministan Iraki, Haidar Al-Abadi REUTERS/Hadi Mizban/Pool
Talla

Har ila yau jama’ar sun bayana rashin jin dadinsu kan matsalar wutar lantarki da ta addabi kasar kuma sun yi kira da a dau matakin daya dace.

Masu zanga zangar dauke da tutocin kasar a hannayensu sun yi ta wake wake a dandalin Tahir Square, inda suke cewa hukumomin kasar barayi ne.

A bangare guda, babban malami a Kasar, Ayatollah Ali Al-sistani ya yi kira ga Firai ministan Kasar Haidar Al-Abadi da ya dauki tsauraran matakai kan matsalar cin hanci da rashawa tare da fitar da sunayen gurbatattun ‘yan siyasa dake kawo cikas dangane da ci gaban kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.