Isa ga babban shafi
Isra'ila-Gaza

Hamas ta gargadi Isra’ila kan takunkumin Gaza

Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta yi gargadin kaddamar da sabon rikici a Gaza muddin Isra’ila ta ki cire takunkumin zirga zirgar jama’ar da kakakabawa Yankin mai dauke da mutane 25,000.

Mayakan Hamas da ke iko a Gaza
Mayakan Hamas da ke iko a Gaza REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Mahmud Zahar, daya daga cikin shugabannin kungiyar ya ce sakonsu ga Isra’ila a bayyana ne ya ke, ba domin ba za su amince da shirin ci gaba da rufe Yankin na shekaru 9 ba.

Zahar ya ce ba za su cigaba da rike mutanen da aka kashewa iyaye, ‘yaya da kuma lalatawa gidaje ba, ganin yadda suka kwashe makwanni biyu suna samun horon soja da amfani da makamai.

Kimanin Falasdinawa 2,200 Isra’ila ta kashe, yayin Hamas ta kashe Yahudawa 73 a rikicin da bangarorin biyu suka shafe kwanaki 50 suna musayar wuta a a tsakanin watan Yuli zuwa Agusta a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.