Isa ga babban shafi
India

Mutane 27 sun mutu a hatsarin jiragen kasa biyu a india

Hukumomin Kasar India sun tabbatar da mutuwar mutane kimanin 27 yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon kauce hanya da wasu jiragen kasa biyu suka yi lokacin da suke kokarin tsallaka wata gada da ambaliyar ruwa ya lalata a Jihar Madhya Pradesh.

Ana ci gaba da aikin ceto mutane a hatsarin jiragen kasa biyu a jihar Madhya Pradesh kasar India
Ana ci gaba da aikin ceto mutane a hatsarin jiragen kasa biyu a jihar Madhya Pradesh kasar India REUTERS
Talla

‘Yan Sanda sun ce an yi nasarar ceto daruruwan fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su amma wasunsu da dama suka samu raunuka.

Jiragen kasa na daga cikin hanyar sufuri mafi sauki a kasar India.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da garin Harda a cikin dare kusan karfe 12.

Yanzu haka gwamnatin Firaminista Nerendra Modi ta bukaci gudanar da binciken musabbabin faruwar hatsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.