Isa ga babban shafi
UAE

Za a gurfanar da wasu mutane dake kokarin kafa kungiyar Jihadi a daular Larabawa

Hadadiyar daular larabawa za ta gudanar da shari ‘a kan wasu mutane 41 da aka cafke, a kokarinsu na hambaran da gwamantin kasar da nufin kafa kungiyar Jihadin a cikin kasar.

Shugabanin kasashen yankin larabawa Gulf a wani taro kan batutuwan tsaro
Shugabanin kasashen yankin larabawa Gulf a wani taro kan batutuwan tsaro REUTERS/Christophe Ena/Pool
Talla

Wadanda ake zargi sun hada da wasu ‘yan asalin kasar da kuma baki ‘yan kasashen waje da ke shigowa kasar, a kokarinsu na kafa wata kungiyar mai sunan Takfiri domin kafa na su daular Islama irin wanda ISIL da ke haifar da barazanar tsaro a wasu yankuna laraba ke koakrin yi.

Rahotannin sun ce ba a fiya samu ayyukan ta'addanci a cikin kasar ba, sai dai kuma ana zargin mutane na samu umarni daga wasu kungiyoyin Jihadi da ke neman hanyar kutsawa kasar domin tayar da zaune tsaye.

Ana dai zargin wadanda ake tuhuma da alaka da al-qaeda ko mayakan ISIL.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.