Isa ga babban shafi
India-Bangladesh

India da Bangladesh sunyi musayar yankunan da suke rikici a kai

Yau Asabar jama’a sun yita shagulgula a kan iyakokin kasashen Bangladesh da India, bayan da kasashen nasu suka yi musayar wasu kananan tsibiran da suka shafe kusan shekaru 70 suna takun saka a kai. Lokacin da aka cika karfe 12n dare agogon yankin, mutanen da suka shafe shekaru babu makarantu, asibitoci da ma wutar lantarki, sun barke da sowar farin cikin komawa wata kasar ta daban. 

Fraiministan klasar India Narendra Modi tare da takwararsa ta Bangladesh, Sheikh Hasina lokacin da suke kulla yarjejeniyar a cikin wat Yuni
Fraiministan klasar India Narendra Modi tare da takwararsa ta Bangladesh, Sheikh Hasina lokacin da suke kulla yarjejeniyar a cikin wat Yuni REUTERS/Rafiqur Rahman
Talla

Indiya da Bangladesh sun mika wa juna Tsibirai 162 dake gewaye da juna, inda India ta mika wa Bangladesh tsibirai 51, ta karbi 111.
Dama cikin wannan watan kasashen 2 suka ji ra’ayoyin jama’a, game da kasar da suke fatan ci gaba da zama, kuma cikin watan Nuwamba za a mayar da wadanda a halin yanzu, suke a kasar da ba cikinta suke sha’awar ci gaba da zama ba.

A cikin watan Yuni shugabannin kasashen 2 suka kulla yarjejeniya kan mika yankunan ga kasashen nasu.
Wannan matakin ya kawo karshen daya daga cikin rigingimun kan iyaka, da suka fi dadewa a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.