Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta nada sabon shugaba

Kungiyar Taliban ta sanar da nada sabon shugaba mai suna Mollah Akhtar Mansour domin maye gurbin Mollah Umar wanda aka ce ya mutu shekaru biyu da suka gabata.

Taliban ta tabbatar da mutuwar shugabanta Mullah Omar
Taliban ta tabbatar da mutuwar shugabanta Mullah Omar AFP PHOTO/ Aref Karimi
Talla

Hakan na nufin Taliban ta tabbatar da mutuwar Mullah Umar da mahukutan Afghanistan suka sanar.

Bayanai dai na nuni da cewa sabon shugaban kamar dai wanda ya gabace shi, an haife shi ne a farkon shekarun 1960 dukkaninsu a yankin Kandahar yankin da ake kallo a matsayin babbar cibiyar Taliban a kasar Afghanistan.

Ko ya Makomar zaman lafiya a Afghanistan bayan fitar da labarin mutuwar shugaban na Taliban ?

Ana dai hasashen akwai yiyuwar rincabewar matsalar tsaro a Afghanistan sakamakon sanar da mutuwar shugaban Taliban Mullah Omar a ranar Laraba.

Tun a 1990 lokacin yakin basasa a Afghanistan Mullah Omar ke jagorantar Taliban, kuma Mutuwarsa za ta kasance babbar hasara ga Taliban.

Amma Ana ganin labarin mutuwarsa zai kara harzuka mayakan.

Masu nazari na ganin mutuwar Mullah Omar na iya haifar da rabuwar kai tsakanin mabiyan Taliban, musamman zaben wanda zai gaje shi a matsayin jagoran kungiyar.

Kuma mutuwarsa yanzu ta jefa alamar tambaya ga tattaunawar zaman lafiya da Pakistan ke jagoranta tsakanin Taliban da Afghanistan.

Yanzu haka an dage zaman tattaunawar da bangarorin biyu suka shriya gudanarwa a yau Juma’a saboda mutuwar Mullah Omar.

Kuma yanzu ba lalle bane sabon shugaban Taliban ya amince da tsarin tattaunawar zaman lafiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.