Isa ga babban shafi
Afghanistan

Shugaban Taliban Mulla Omar ya rasu

Gwamnatin kasar Afghanistan ta tabbatar da mutuwar shugaban kungiyar Taliban Mullah Omar bayan mai magana da yawun hukumar leken asirin kasar Hasseb Sediqi ya bayar da sanarwar, inda yace cikin shekarar 2013, Mullah Omar ya mutu a wani Asibitin birnin Karachi, na kasar Pakistan.

Wikipedia/Unknown
Talla

Tun cikin shekarar 2001, rabon da a ga Mullah Omar a bainar jama’a, lokacin da Amurka ta jagoranci hare haren da aka kai Afghanistan, inda aka hambarar da gwamnatin ‘yan Taliban ta wancan lokacin.

Mai magana da yawun shugaban kasar ne ya bayyana cewa hukumomin kasar suna tunanin Mulah Omar ya dade da mutuwa.

Zuwa yanzu kungiyar Taliban ba ta ce uffam ba kan batun, sai dai ana sa ran nan gaba kadan za su fitar da sanarwa a kai.

A baya an yita yada jita jitar rashin lafiya, da mutuwar shugaban na Taliban, sai dai rahotannin baya bayan nan na zuwa kwanaki 2 kawai, kafin wani zagayen tattaunawa tsakanin mayakan na Taliban, da mahukuntan birnin Kabul.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.