Isa ga babban shafi
Iran

Kudaden ajiyarmu ba su kai yadda aka kiyasta ba- Iran

Babban bankin kasar Iran ya ce adadin kudade dala Biliyan 29 na kadarorin kasar ne ke je a kasashen waje sabanin dala biliyan 100 da aka kiyasta a baya.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani REUTERS
Talla

Iran za ta samu damar amfani da kudadenta na ajiya a waje karkashin yarjejeniyar Nukiliya da kasar ta amince da manyan kasashen duniya guda 6.

Shugaban babban bankin na Iran ya ce Bankin na da adadin kudade dala biliyan 23, yayin da gwamnatin Iran ke da adadin kudi dala biliyan 6.

Isra’ila babbar mai adawa da Iran ita ce ta yi kiyasin cewa Iran ta mallaki kudade dala biliyan 100 a asusun ajiyarta na waje, wanda ta ke ganin ba Iran damar mallakar kudaden zai kara wa kasar karfi a gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.