Ana kama dan kasuwan kasar Cambodia da ya ci zarafin wata mace
Yau Asabar ‘yan sandan kasar Cambodia suka kama wani hamshakin dan kasuwa da ake nema ruwa a jallo, bayan da aka aka nuna shi cikin wani hoton Bidiyo yana dukan wata mace mai gabatar da shirin gidan Talibijin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tun lokacin da hoton ya bayyana, jama’a suka yi ta bayyana bacin ransu a kai, lamarin da ya sa Jami’an tsaro ke neman dan kasuwan mai suna Sok Bun, ruwa a jallo.
Bayan fara neman sa ne Sok ya tsere zuwa kasar Singapore, sai dai a loacin da ya dawo kara yau Asabar jami’an tsaro suka cafke shi a filin jirgin samana Phnom Penhm inda aka tasa keyar sa.
Hotunan Bidiyon sun nuna dan kasuwan mai shekaru 37 a duniya, dake harkar gine gine, yana dukan Ek Socheata, da aka fi sani da sunan SaSa, a wani wajen cin abinci.
Masu gabatar da kara sun ce mutumin ya amsa laifin, kuma yanzu haka ana tsare da shi a wani gidan yarin dae Prey Sar, inda zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 5 kan laifin.
Dama ana gani kasar ta Cambodia a matsayin inda inda masu hannu da shuni ke take doka ba tare da bangaren shari’a ya iya yin wani abu ba a kai, kuma cin zarafin mata abu ne da ya zama ruwan dare a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu