Isa ga babban shafi
Armenia

Shugaban Kasar Armeniya ya dakatar da karin kudin wuta

Shugaban Kasar Armeniya, Serzh Sargsyan ya dakatar da Karin kudin wutar lantarki da Kasar ta yi, bayan jama’a sun yi bore dangane da Karin kudin.

Shugaban Armenia, Serzh Sargsyan
Shugaban Armenia, Serzh Sargsyan REUTERS/Mike Segar
Talla

To sai dai duk da kokarin shugaban na dakatar da karin, hakan bai gamsar da masu boren ba yayin da suka lashi takobin ci gaba da zanga zangar nuna adawa ga gwamnatin Kasar.

A kwana kwanan ne Gwamanatin ta yi Karin kashi 16 cikin 100 na kudin wutar lantarki, lamarin da ya tunzura dubban jama’a bazama kan titunan Yerevan babban birnin Kasar don nuna rashin amincewar su da matakin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.