Isa ga babban shafi
Yemen-Morocco

Huthi ta kakabo Jirgin yakin Moroko a Yemen

Jiragen kasashen gamaya sun kai wani munmunar hari akan wajen ajiyan makamai a Sana’a babban birnin kasar Yemen, Wannan kuwa na zuwa ne adai-dai lokacin daya rage sa’o’i kadan a soma aiki da dokar tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu.

'Yan tawayen Yemen
'Yan tawayen Yemen REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

‘Yan tawayen Huthi sun kuma dauki alhakin kai harin akan jirgin yakin mallakin kasar Moroko wanda kuma ya kasance jirgin farko da aka kakkabo tun soma yakin

Rikicin dai na cigaba da kazancewa sanadiyar yadda kasar saudiya ke kai hare hare a yankunan ‘yan tawayen yayin da bangaren ‘yan tawayen Huthi ke cigaba da mayar da martani, ta hanyar harba rokoki acikin kasar Saudiya.

kawo yanzu dai babu alamar dakatar da wadanan hare haren da ke cigaba da salwantar da rayukan al’umma da dukiya a kasar ta Yemen

ko a jiya lahadi rahotanin a kasar na cewa an kai wani munmunar hari gidan tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh yayin da mutane goma sha tara suka rasa rayukansu a birnin Aden.

A gobe talata ne ake saran soma aiki da dokar tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki biyar da aka cimma domin samun damar sauke kayayakin agaji

Akalla mutane dubu 1400 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar rikicin a watan Maris da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.