Isa ga babban shafi
Nepal

Mummunar Girgizan kasa ta abka wa Nepal

Mutane sama da 4,000 aka ruwaito sun mutu sakamakon wata mummunar girgizan kasa da ta abkawa sassan yankunan Nepal tun a ranar  Assabar. Hukumomin kasar sun ce adadin wadanda suka mutu na iya zarce haka anan gaba saboda akwai daruruwan mutane da gini ya rubta da su sakamakon girgizan kasar.

Girgizan kasa a Nepal ta rusa gidaje da katse lantarki
Girgizan kasa a Nepal ta rusa gidaje da katse lantarki REUTERS/Navesh Chitrakar
Talla

Girgizan kasar mai girman maki 7.8 ta shafi yankunan Kathmandu babban birnin Nepal da wasu yankuna zuwa tsaunin Everest kusa da yankin India da Bangladesh.

Kungiyoyin agaji daga kasashen duniya da dama na ci gaba da kai dauki zuwa kasar Nepal bayan daruruwan mutane sun mutu.

Rahotanni sun ce girgizan kasar ta lalata hanyoyin sadarwa da kaste wutar lantarki tare da lalata hanyoyin ababen hawa lamarin da kuma ke kawo tarnaki ga aikin jami’an agaji.

Tuni dai Amurka da Faransa da kungiyar Tarayyar Turai suka aika da Jami’an agaji da kudaden tallafi zuwa Nepal.
 

Yanzu haka gwamnatin Nepal ta kafa dokar ta-baci a yankunan da girgizan kasar ta shafa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.