Isa ga babban shafi
Sri Lanka

An tsare kanin tsohon Shugaban Sri Lanka

Wani alkali a kasar Sri Lanka ya bada umurnin tsare kanin tsohon shugaban kasar Mahinda Rajakpase saboda zargin da ake masa na rub da ciki da kudaden talakawa

Tsohon Shugaban Kasar Sri Lanka, Mahinda Rajapaksé
Tsohon Shugaban Kasar Sri Lanka, Mahinda Rajapaksé EUTERS/Dinuka Liyanawatte
Talla

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan tsohon shugaban Kasar ya zargi gwamnatin yanzu da cin zarafin ‘Yan adawa.

Ana tuhumar Basil Rajapakase wanda tsohon ministan tattalin arzikin kasar ne, da bacewar Dalar Amurka dubu 530, kudin da aka ware dan samar da gidaje ga jama’ar kasar.

Alkalin ya bada umurnin tsare tsohon ministan na makwanni biyu bayan shafe tsawon awanni 7 yana amsa tambayoyi.

A dayan bangaren, rahotannin sun nuna cewa, shi kanshi tsohon Shugaban Kasar da yiwuwar ya fuskanci tuhuma a gobe Jumma’a bisa zargin sa da laifin cin hanci da rashawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.