Isa ga babban shafi
Taiwan

Jirgin saman Taiwan ya yi hatsari

Akalla mutane 11 aka tabbatar da mutuwarsu bayan wani jirgin TransAsia na Taiwan ya yi hatsari a cikin wani Rafi da ke kusa da Taipei babban birnin kasar. Rahotanni sun ce Ma’aikatan agaji na ci gaba da kokarin kubutar da rayukan mutane sama da 30 da suka makale a cikin jirgin.

Hoyon Bidiyo ya nuna yadda Jirgin Taiwan na TransAsia ya yi hatsari
Hoyon Bidiyo ya nuna yadda Jirgin Taiwan na TransAsia ya yi hatsari Capture d'écran Youtube
Talla

Jirgin wanda ke jigila a tsakanin biranen Taiwan, yana dauke ne da Fasinja kusan 60. Na’urar hoton bidiyo ta nuna yadda jirgin ya bugi gada kafin ya fada cikin wani rafi.

Hatsarin kuma ya faru ne da safiyar Laraba bayan jirgin mai lamba ATR 72-600 ya tashi daga tashar jirgin sama ta Songshan a arewacin Taipei zuwa lardin Kinmen.

Hukumomin Taiwan sun ce kimanin mutane 16 suka samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.