Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 27/02 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 27/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 27/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 27/02 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 27/02 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 27/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Asiya

An fara tattaunawa da masu zanga zangar Hong Kong

media Masu zanga zanga tare da 'yan sanda a Hong Kong REUTERS/Tyrone Siu

Hukumomin birnin Hong Kong suka hau teburin sasantawa, da masu zanga zangar neman ganin an tabbatar da tsarin democradiyyar a yankin. Ana sa rai tattaunawa ta yau Talata zata kawo karshen gangamin da aka shafe makonnin ana yi a kan titunan birnin, lamarin da kawo tsaiko a harkokin yau da kullunm.
Wannan na zuwa ne sa’oi kadan baya Shugaban yankin Hong Kong Leung Chun-ying, yace zaben da za a gudanar zai baiwa talakawa damar shiga a dama dasu a harkokin siyasa yankin.
Cikin wata hira da yayi da kafafen yada labarum kasashen waje, Chun-ying, dake ci gaba da fuskantar matsin lamba, ya sake jaddada matsayin shi kan zai yi wuya a sami gudanar da tsaftataccen zabe a yankin.
Yau fiye makonni 3 kenan, da masu zanga zangar suka rurrufe manyan titunan birnin na Hong Kong dake kudancin kasar China, inda suke neman a inganta tsarin democradiyya a yankin.
Zanga zangar na da nasaba da karuwar rashin daidaito tsakanin al’umma, da kuma tsadar rayuwa da jama’a ke kara shiga.
Duk da cewa zanga zanga na gudana cikin lumana, sai dai kuma an samu tashe tashen hankula a wasu wuraren, lokacin da ‘yan sanda suka yi yunkurin bude hanyoyin da aka rurrufe.
Wannan kuma na matsayin daya daga cikin kalu bale mafi girma da hulumomin birnin Beijing ke fuskanta, tun bayan gangamin neman tabbatar da tsarin democradiyya, da aka yi cikin shekarar1989 a dandalin Tiananmen.
 

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure