Isa ga babban shafi
Hong Kong

Masu zanga zangar neman mulkin demokradiya a Hong Kong na ci gaba da mamaye manyan tinunan birnin

SHUGABAN Gudanarwar Hong Kong Leung Chun-ying ya bukaci masu zanga zanga a kasar da su janye magoya bayansu daga kan tituna kamar yadda suka yi alkawari yi kafin fara ta.

Yan sanda sun killace masu zanga zanga a kan titunan à Hong Kong  30 septamba  2014.
Yan sanda sun killace masu zanga zanga a kan titunan à Hong Kong 30 septamba 2014. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Su dai masu zanga zangar sun ci gaba da zaman dirshen a titunan kasar a fafutukarsu na ganin China ta aiwatar da tsarin mulkin demokradiya a Ynakin.

Daya daga cikin masu zanga zangar Chan Kin-man yace idan shugaban Yankin ya sauka daga mukaminsa zasu dakatar da zanga zangar da suke yi.

Yankin na Hong Kong dai da a baya ya zauna a karkashin jagorancin kasar Ingla na tsawon shekaru 100 kafin komawarsa ga hannu China na fama da rikice rikicen mulki ne bayan da mazana yankin suka nemi kasar ta China da ta ci gaba da aiwatar da tsarin demokradiyar da kasar Ingla ta jagoranci yankin da shi>
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.