Isa ga babban shafi
India

Al Qaeda ta bude reshe a India

Shugaban Kungiyar Al Qaeda Ayman al Zawahiri ya bayyana kafa wani sabon reshe a Yankin India a wani sakon bidiyo da ya aika wa duniya. Zawahiri yace reshen zai kawar da iyakokin da aka shata a nahiyar da ke raba al’ummar Musulmi.

Shugaban Kungiyar Al Qaeda Ayman Zawahiri
Shugaban Kungiyar Al Qaeda Ayman Zawahiri REUTERS
Talla

Kungiyar Al Qaeda tana da magoya baya sosai a Afghanistan da Pakistan inda ake saran a tsakanin kasashen ne shugabanin kungiyar ke rayuwa.

Sakon bidiyon na tsaron minti 55 ya fara ne da nuna Marigayi Osama bin Laden yana gabatar da huduba.

A cikin sakon Bidiyon, Zawahiri yace kungiyar za ta kaddamar da hare hare a India da Myanmar da Bangladesh.

Zawahiri yace zasu ci gaba da jihadin shugabansu da Amurka ta kashe Osama bin Laden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.