MH17 : Ana zaman makoki a Malaysia
Al’ummar kasar Malaysia suna zaman makoki bayan isowar gawarwakin mutane 20 cikin wadanda suka mutu a hadarin jirgin kasar MH17 da ya tarwatse a kasar Ukraine. Sarki Abdul Halim Mu’adzam Shah tare da Firaminista Najib Razak ne suka jagoranci jami’an gwamnati a filin jirgin saman birnin Kuala Lumpur, domin karbar gawarwakin.
Wallafawa ranar:
Jirgin kamfanin Jiragen saman kasar Malaysia mai lamba MH17 dauke da mutane 298, ya tarwatse ne a lardin gabacin kasar Ukraine, a wani yanayin da ake ganin harbo jirgin aka yi a kasar mai fama da rikici a ranar 17 ga watan Yulin da ya gabata.
An dakatar da bukukuwa a kasar Malaysia tare da sassauto da tutar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu