Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Ana ci gaba da musayar Wuta tsakanin Israela da Paledinu

Hare haren da sojojn Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a cikin dare akan garuruwan da ke yankin Gaza, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 100 yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka, kamar yadda mai Magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiya a yankin na Gaza Ashraf Al-Qudra yake cewa

Talla

Ya ce sojan saman Gaza, sun kai hare haren ne a yankin Rafah da rana yayin kwmatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a jiya alhamis amma ba tare da ya fitar da wata sanarwa ba.

Kungiyar Hamas kuwa na can tana ta aman Rokoki a tsakkiyar Isra'ila, sai dai uya zuwa yanzu ba'a bayyana yawan mutanen da Hamas ta kashe daga bangaren Isra'ila ba.

Rahotanni sun ce ana ta jin rugugin Rokoki daga bangaren Palesdinu masu maida martani akan kisan gillar da Isra'ila ke kai masu.

A jimilce dai fararen hula 100 ne suna rasa rayukansu a jerin hare-hare fiye da 750 da da sojin Isra’ila suka kai wa yankin na Gaza a cikin wadannan kwanaki 4 da suka gabata.

Taron da Kwamitin tsaro na MDD ya kira a jiya alhamis domin tattaunawa kan wannan batu, ya kawo karshe ba tare da an fitar da wata sanarwa ba, amma babban magakatardan Majalisar Ban Ki-moon, ya bukaci Isra’ila da ta tsagaita wuta domin ceton rayukan fararen hula.

Fadar shugaban Amurka ta White House kuwa, ta bayyana cewa an tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Barack Obama da Benyamin Netenyahu na Isra’ila a cikin daren jiya, kuma Obama ya ce a shirye yake ya nemi Isra’ila ta tsagaita wuta, duk da cewa ya bayyana hare-haren na Isra’ila a matsayin na kare kai ne .

Wasu rahotanni da dumiduminsu kuwa, sun bayyana cewa wani makami mai linzame da aka harbo daga arewacin kasar Lebanan, ya fada a cikin Isra’ila da sanyin safiyar yau, sai dai babu cikakkun bayanai game da irin hasarar da ya haddasa, yayin da a kasar Maroko, ake shirin gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna goyon bayan ga Palasdinawa a yau juma’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.