Isa ga babban shafi
Japan

Guguwar Noegui ta afka wa kudancin kasar Japan

Hukumomi a kasar Japan na ci gaba da samar wa jama’a mafaka sakamakon yadda guguwar Neogui da ke tafiyar kilomita 270 a cikin sa’a daya ta doshi tsibirin Okinawa da ke kudancin kasar.

Guguwar noegui a Japan
Guguwar noegui a Japan
Talla

Tun a karshen makon da ya gabata ne jami’an hukumar hasashen yanayi suka yi gargadin cewa guguwar za ta iya haifar da mummunan bala’i ga kasar, domin kuwa za ta iya shafar akalla mutane milyan daya da dubu 200.

Kawo yanzu dai an kwashe mutane sama da dubu dari hudu zuwa wasu wurare domin ba su kariya. Masana dai na bayyana Neogui a matsayin guguwar da ta yi kama da Haiyan wadda ta afka wa kasar Philippines har ma aka samu asarar rayukan mutane dubu 7 da 300 a cikin watan nuwambar bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.