Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Amurka da MDD sun ce lokaci na kurewa Iraqi

Kasar Amurka da Majalisar Dinkin Duniya, sun ce lokacin yana kurewa ganin yadda aka kasa cim ma matsaya a Majaliar dokokin kasar game da batun kafa gwamnatin hadin kai.

Mayakan Sunni dake tayar da kayar baya a Iraqi
Mayakan Sunni dake tayar da kayar baya a Iraqi
Talla

An dai samu baraka a zaman farko na majalisar kasar ta Iraqi wacce kasashen duniya da dama ke tunanin za ta kawo karshe rikicin kasar.

“Lokaci na kurewa Iraqi, akwai bukatar a samar da mafita cikin gaggawa.” Inji Kakakin ma’aikatar kasar Amurka, Marie Harf.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan rikicin kasar ta Iraqi, Nickolay Mladenov ya ce akwai bukatar ‘yan siyasar kasar su gane cewa yanzu al’amura ba kamar da bane.

Kusan makwanni biyu da suka gabata kasar ta Iraqi ta fada cikin rikici bayan da mayakan Sunni suka karbe wasu yankunan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.