Isa ga babban shafi
Saudi

Azumi : Saudiya ta dauki matakai akan wadanda ba Musulmi ba

Hukumomin kasar Saudiya sun yi kira ga wadanda ba Musulmi ba su kauracewa fitowa bainar Jama’a suna cin abinci ko zukar taba sigari a lokacin da Musulmi ke gudanar da Azumin watan Ramadan, Gwamnatin Saudiya tace zata dauki matakan korar duk wanda ya sabawa masu Azumi.

Wani dan kasar Saudiya ya kasa Dabino a kasuwa kafin soma Azumin watan Ramadan a yankin Utaiqah da ke kudu da birnin Riyath.
Wani dan kasar Saudiya ya kasa Dabino a kasuwa kafin soma Azumin watan Ramadan a yankin Utaiqah da ke kudu da birnin Riyath. REUTERS/Faisal Al Nasser
Talla

Ma’aikatar cikin gida a Saudiya ta yi kira ga wadanda ba Musulmi ba a kasar su kauracewa fitowa suna cin abinci a bainar Jama’a.

A cikin sanarwar da Kamfanin dillacin labaran kasar ya ruwaito, Gwamnatin Saudiya tace don mutum ba Musulmi ba ne wannan ba dalili ba ne domin akwai mutunta ‘Yancin musulmi a cikin dokar aiki a kasar.

Gwamnatin Saudiya tace wadanda suka saba ana iya korarsu daga aiki tare sallamarsu daga kasar.

Azumin watan Ramadan, yana cikin shika shikan Musuluci kuma Al’ummar Musulmi sukan kauracewa ci da sha da saduwa da iyali tun daga fitowar al fijir har zuwa faduwar rana.

A kasar Saudiya mai arzikin fetir akwai Miliyoyan mutane ‘yan kasashen waje da ke aiki a kasar yawancinsu mutanen China da Japan da wasu kasashen yankin Asiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.