Isa ga babban shafi
China-Vietnam

An kwashe Sinawa sama da dubu uku daga Vietnam

Hukumomin kasar Vietnam sun baza dimbin jami’an tsaro domin bai wa ‘yan asalin China da ke zaune kasar kariya, bayan da al’ummar kasar suka kaddamar da boren nuna adawa da ‘yan kasar ta Sin.

Masu zanga-zanga a kasar Vietnam
Masu zanga-zanga a kasar Vietnam 路透社
Talla

Yanzu haka dai ‘yan asalin China biyu ne suka rasa rayukansu tare da raunata wasu 135, lamarin da ya tilasata wa hukumomin birnin Beijing kwashe Sinawa sama da dubu uku daga kasar domin mayar da su gida.

‘Yan kasar ta Vitnam sun tayar da wannan bore ne bayan da ma’aikatan wani kamfanin hako mai na China suka fara aiki akan wasu tsibirai da kasar ta Vietnam ke ikirarin cewa mallakinta ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.