Isa ga babban shafi
China-Vietnam

Ana zanga-zangar kin jinin China a Vietnam

Rahotanni sun ce an samu mutuwar mutum guda yayin da sama da 100 suka samu raunika a zanga zangar kin jin jinin China da ake gudanarwa a kasar Vietnam. Rahotannin kuma sun ce akwai masana'antu kasar China sama da 12 da aka cinnawa wuta saboda wata takaddama da ta kaure a tsakanin kasashen biyu kan rijiyar mai.

Zanga-zangar kin jininin China a Vietnam
Zanga-zangar kin jininin China a Vietnam @Google
Talla

Yanzu zanga-zangar ta bazu zuwa yankunan kasar Vietnam 22 cikin 63.

Matakin sanya wuta akan kamfanoni mallakar kasar China ya dada fito da tankiyar da ke tsakanin kasashen biyu, inda masu zanga zangar suka dinga dibar ganima daga masana'antun.

Wani Dan kasar Taiwan da ya sha da kyar, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, masu zanga zangar sama da 20,000 cikin fushi sun kona kamfanoni da dama, mallakar kasahsen Taiwan da Koriya ta kudu da China, yayin da wasu kuma cikin tsoro suka rufe masana'antunsu suka gudu.

Hukumomin kasar daga bisani sun girke jami'an tsaro masu kwantar da tarzoma don magance tashe tashen hankulan. Kasar China ta bukaci yin taka tsan-tsan dangane da tashin hankalin.

Kasashen Vietnam da China d sun dade suna takaddama kan mallakar wasu tsibirai masu arzikin mai a kudancin ruwan China inda kowacce kasa ke cewa na ta ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.