Isa ga babban shafi
Malaysia-China

An ci gaba da laluben jirgin kasar Malaysia a tekun India

Yau Juma’a kasashe dake laluben tekun India, don gano jirgin saman Malaysia da ake zaton ya fada ciki, sun koma neman jirgin bayan tsaikon da aka samu na wani dan lokaci, saboda gurbacewar yanayi.A gobe mako uku kenan chur da faduwan jirgin da mutane 239, fiye da rabi ‘yan kasar China, kuma har yanzu babu bayani takamaime, kan ainihin inda ya fada a cikin tekun.Masu bincike a kasar Thailand sun bada sanarwan hango wasu tarkace na yawo a tekun, kuma masu bincike sun bazama don ganin ko wasu sassan jirgin da ake nema ne.Dama Gurbacewar yanayi ya sa aka dakatar da aikin neman jirgin.Bayanai na cewa jiragen ruwa dana sama dake aikin neman inda jirgin ya fada a tekun India sun fuskanci matsanancin yanayi da isk , da ala tilas a jinkirta aikin. 

Hoton wurin da ake tunani jirgin kasar Malaysia ya fada a tekun India。
Hoton wurin da ake tunani jirgin kasar Malaysia ya fada a tekun India。 REUTERS/Malaysian Remote Sensing Agency/Handout via Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.