Isa ga babban shafi
Malaysia-Vietnam

Vietnam ta dakatar da aikin neman jirgin Malaysia da ya bace

Hukumomin kasar Vietnam sun sanar da kawo karshen neman jirgin saman Malaysia da ya bace da mutane sama da 200, har sai sun samu wasu bayanai daga kasar Malaysia.

Mataimakin rundunar Sojan saman kasar Vietnam Laftanal Nguyen Tri Thuc yana aikin binciken jirgin kasar Malaysia MH370 da ya bace
Mataimakin rundunar Sojan saman kasar Vietnam Laftanal Nguyen Tri Thuc yana aikin binciken jirgin kasar Malaysia MH370 da ya bace REUTERS/Kham
Talla

Jami’an Malaysia suna tunanin jirgin ya karkata akalarsa ne bayan tashinsa daga Kuala Lumpur zuwa birnin Beijing.

Yanzu haka dai gwamnatin Malysia na fuskantar suka musamman game da bayanai masu karo da juna a ci gaba da aikin gano jirgin.

Shugaban ‘Yan Sandan kasar Malaysia Janar Khalid Abu yace akwai matsaloli da suka gano a bincikensu da suka shafi fashi da zagon kasa da matsala daga masu kula da jirgin da fasinjoji da kuma matsala daga matuka jirgin.

Jirgin saman wanda gwamnatin Vietnam ta ce ya bata ne a sararin samaninyarta bayan ya taso daga Kuala Lumpur fadar gwamantin Malaysia zuwa Beijing na kasar China a ranar Assabar ta makon jiya, har yanzu babu wasu bayanai da ke tabbatar da hakikanin abin da ya faru da shi.

Gwamnatin Malaysia ta danganta bacewar jirgin da wani yunkuri na ta’addanci yayin da jami’an tsaro suka ce akwai wasu ‘Yan kasar Iran akalla 2 a cikin jirgin tare da Faspon da suka sace.

Sai dai hukumar ‘Yan sandan kasa da kasa ta Interpol tana tunanin bacewar jirgin ba ya da alaka da ta’addanci, sai dai kuma akwai satar bayanan hukumar da aka yi a cewar shugabanta Ronald Noble.

Amma Hukumar leken asirin Amurka CIA ta ce ko shakka babu bacewar jirgin na da nasaba da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.