Isa ga babban shafi
China

China ta kashe wani mutum akan laifin Fyade ga Mata

Hukumomi a kasar China, sun zartas da hukuncin kisa akan wani mai suna Li Hao mai shekaru 35 a Duniya, bayan da aka sameshi da laifin yin garkuwa da wasu mata 6 da kuma yi masu fyade a tsawon watanni 21 da yake rike da su

zartas da hukuncin kisa a China
zartas da hukuncin kisa a China theepochtimes.com
Talla

Kotu a China ta ce 5 daga cikin wadanda ya yi garkuwa da su mata ne masu zaman kansu da ke da shekaru 16 zuwa 23 a Duniya, wadanda ya tsare a wasu dakuna kafin a gano shi.

Daga cikin wadanda yayiwa Fyade dai akwai masu Shekaru daga 16 zuwa 23, akwai kuma mai Shekaru 20 da ta dauki Ciki.

Mutumin haka ma ya tilastawa 3 daga cikin Matan da su kashe 2, kuma ya taba aika Hoton Bidiyo na lalatar da yayi da su a Yanar Gizo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.