Maldives
Kotun kolin Maldives ta haramta gudanar da zaben shugaban kasa
Kotun kolin kasar Maldives, a yau lahadi ta haramta gudanar da zaben shugabancin kasar zagaye na biyu, a daidai lokacin da hambararren shugaban Mohamed Nasheed ke kyautata zaton samun nasara domin sake dawowa a kan mukaminsa.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan ne dai karo na uku da kotu ke haramta gudanar da zaben, lamarin da ke neman jefa wannan karamar kasa da ke tekun India a cikin wani mummunan rudani na siyasa.
A karshen makon da ya gabata hukumomin kasar sun tabbatar da cewa za a gudanar da zaben, lamarin da ya cutura bayan hukuncin kotun kolin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu