Isa ga babban shafi
Cambodia

Dubban 'Yan adawa suna zanga-zanga a Cambodia

Dubban mutane ke ci gaba da gudanar da zanga zanga a kasar Cambodia, saboda zargin da suke cewar an tafka magudi a zaben kasar, don bai wa Firaminista Hun Sen damar ci gaba da zama a karagar mulki.

Sam Rainsy madugun adawa yana jagorantar zanga-zangar adawa da zaben Cambodia
Sam Rainsy madugun adawa yana jagorantar zanga-zangar adawa da zaben Cambodia REUTERS/Samrang Pring
Talla

Shugaban ‘Yan adawar kasar, Sam Rainsy ya bukaci magoya bayansa sama da 100,000 da suka fito, da su ci gaba da zanga zanga, dan kwato kuri’un su.

Dubban mutane ne suka fito saman tituna dauke suna daga tuta tare da yayata kalaman neman sauyi.

Amma akwai ‘Yan sanda masu kwantar da tanzoma da aka girke a dandalin masu zanga-zangar.

‘Yan adawa dai suna neman a kaddamar da bincike akan magudin zabe da suke zargin an tabka kuma Jam’iyyar adawa tace zata kai kokenta zuwa ga ofishin jekadancin kasashen Turai da suka hada da Faransa da Birtaniya da Amurka domin kwato masu hakkinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.