Isa ga babban shafi
Indiya

Yara 20 sun mutu a India bayan sun ci abinci mai guba

Yaran makarantar Firamare 20 sun mutu a kasar Indiya, bayan sun ci wani abinci mai guba, yayin da wasu da dama suka kamu da rashin lafiya, a wani kauyen Masrakh da ke yankin gabacin kasar. Tuni Gwamnatin kasar ta kaddamar da bincike kan lamarin, yayin da ta biya diyyar Dala 3,370 ga iyalan daliban da suka rasu.

Wani Hoton Bidiyon yaran da suka ci guba a kasar India
Wani Hoton Bidiyon yaran da suka ci guba a kasar India Reuters
Talla

Hukumomin Ilimi a Jahar Bihar sun ce kimanin yara 30 ne yanzu kwance a gadon Asibiti bayan yaran sun ci abincin rana a makarantar.

Daliban wadanda shekarunsu bai haura 10 an binne su ne a kusa da makarantar amma akwai daruruwan mazauna kauyen Masrakh da suka fito suna zanga-zanga sakamakon mutuwar yaran.

Binciken da aka gudanar, an gano gubar ta shiga abincin ne ta hanyar maganin kwari amma likitoci na ci gaba da kula da lafiyar yaran da ke kwance a gadon Asibiti.

Sai dai kuma kafafofin yada labaran Indiya sun ruwaito kalaman mazauna kauyen na zargin an yi amfani da gurbataccen mai ne wajen dafa abincin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.