Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Koriya ta Arewa ta yi kira ga ‘Yan kasashen waje su fice kada tsotsayi ya rutsa da su

Kasar Koriya ta Arewa ta roki ‘yan kasashen waje da su fice daga yankunan Koriya ta Kudu don gudun kada tsautsayi ya rutsa da su. Wannan Gargadin na zuwa ne a dai dai wani lokaci da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ke aikawa da gargadi ga Koriya ta Arewa na kaucewa kaddamar da yaki domin ba a san me zai haifar ba.

Dakarun Korea ta Kudu da na amurka da ke shirin kai wa Korea ta Arewa Hari
Dakarun Korea ta Kudu da na amurka da ke shirin kai wa Korea ta Arewa Hari
Talla

Koriya ta Arewa dai ta nemi ‘Yan kasashe waje baki su kama gabansu domin ba za ta iya tattabatar masu za ta iya kare lafiyarsu ba.

Kwamitin sasantawa na Asia-Pacific ya fadi cikin wata sanarwa cewa akwai alamu na zahiri yiyuwar ballewar yaki tsakanin Koriya ta Kudu da koriya ta Arewa ganin yadda suke tayar da jijiyoyin wuya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.