Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Rasha da China za su hau kujerar na-ki kan yunkurin daukan matakin soji akan Korea ta Arewa

Kasashen Rasha da China sun ce za su hau kujerar na-ki ga duk wani kudirin daukar matakin soji akan Korea ta Arewa bayan samun nasarar gwajin harba makamin Nukiliyarta. Wannan kuma na zuwa ne bayan Hukumar Makamashi ta Duniya IAEA, ta ce Iran ta na zangon karshe na kammala shirin mallakar makamin Nukiliya.

Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong Un REUTERS/KCNA
Talla

Duk da ya ke kasashen Rasha da China sun bayyana damuwa game da gwajin makamin Nukiliyar kasar Korea ta Arewa, amma kasashen biyu sun ce za su yi watsi da duk wani kudirin kasashen yammaci da Amurka na daukar matakin soji akan kasar

Wannan kuma na zuwa ne bayan Ministocin harakokin kasashen Biyu na Rasha da China sun yi wata ganawa ta musamman

A watan jiya ne Gwamnatin kasar Korea ta Arewa ta tabbatar da samun nasarar gwajin makamin Nukiliyarta, al’amarin da kasashen Duniya suka yi Allah Wadai da shi.

Tuni Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya kunshi kasashen Rasha da China ya yi alkawarin daukar matakin da ya dace akan kasar Korea ta Arewa, bayan samun nasarar gwajin makamin nukiliyar kasar.

Irin wannan batu ne dai ya shafi kasar Iran inda hukumar makamashi ta Duniya ta tabbatar da cewar kasar Iran ta fara dasa wasu na’urorinta a zangon karshe na kokarin cim ma aikin mallakar makaman Nukiliya.

Kuma amintakar da ke tsakanin Rasha da China da Korea ta Arewa irin ta ce ke tsakanin kasashen Biyu da Iran da ke fuskantar kalubale daga Amurka da kasashen Yammaci.

Yanzu haka kuma Firaminstan Japan Shinzo Abe yana ziyara a Amurka inda zai tattauna da Shugaba Obama dangane da batun Nukiliyar Korea ta Arewa da kuma kazancewar danganta tsakanin China da Japan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.