Kotu ta dage sauraren Shari'ar Fyade a India
Kotu a kasar India ta dage sauraron shari’ar fyade da kuma kisan kai da ake wa wasu matasa biyar, Shari’ar da yanzu haka ke dauke hankalin kasashen duniya. A lokacin zaman kotun mai shari’a ya kori ‘yan jaridu da wasu tarin lauyoyin da suka cika kotun, inda aka saurari shari’ar cikin sirri da kuma kwararan matakan tsaro.
Wallafawa ranar:
Priya Hingorani, mai gabatar da kara a kotun koli, kuma mai fafutukar kare yancin mata, tace suna fatar ganin an kamala shari’ar cikin lokaci, tsakanin watanni biyu zuwa uku.
Yanzu haka dai akwai shari’un fyade da aka kwashe tsawon shekaru tara ana yi, abinda ke ci gaba da harzuka wadanda aka ci zarafin su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu