Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 18/11 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 18/11 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 18/11 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 18/11 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 15/11 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 14/11 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 15/11 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 15/11 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 15/11 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Asiya

wata kotu a Indiya ta ce, gwaje-gwajen magungunna ba kan ka'ida ba a kasar na jawo matsaloli ga koshin lafiyar jama'a

media Getty Images/E+/Savushkin

Kotun kolin kasar India ta ce, gwaje-gwajen sabbin magunguna, ba bisa ka’ida ba, da wasu kamfanonin sarrafa magunguna ke yi, na jawo matsalolin lafiya masu yawan gaske a kasar.

Kotun ta kuma umarci ma’aikatar lafiyar kasar ta rinka sa ido, kan duk wani gwajin sabbin magungunan da za a yi a kasar ta Indiya.
 

Kotun ta dauki wannan mataki ne a yau Alhamis, yayin sauraren koke, kan kan mace-mace, da matsalolin lafiyar da irin wadannan gwaje-gwajen ke janyo wa mutanen da aka yi gwajin kansu, da kuma yawancinsu an yi gwajen ne a kansu ba tare da sani ko amincewar su ba.

Mai shari’a R.M. Lodha yace akwai batutuwa da dama, da suka shafi doka da hankali, da ya kamata hukumomi su kiyaye, amma ake biris da su.

Alkalin, ya kara da cewa, ana amfani da ‘yan kasar ta Indiya tamkar kayan gwajin magunguna, inda ya umarci sakataren lafiyar kasar da ya mayar da hankali sosai kan lamarin.

Masu koken, da suka hada da wata kungiyar likitoci da ‘yan wata kungiyar sa kai, sun ce araha, rashin dokoki masu karfi, da rashin aiki da dokoki, na wasu daga cikin dalilan da ke sa ana irin wadannan gwaje gwajen ba bisa ka’ida ba.

Kungiyoyin sun ce, sun gabatar da wani rahoton da ke nuna yadda aka yi amfani da marasa lafiya fiye da 200, don gwada magunguna, ba tare da izinin su ba.
 

Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure