An rataye dan bindigar Mumbai a Indiya
Hukumomin kasar Indiya sun rataye Mohammed Ajmal Amir Kasab, daya daga cikin ‘Yan bindigar da suka kai hari a Mumbai a shekarar 2008, wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane 166. A yau Laraba ne aka rataye Kasab a gidan yarin Yerwada a Pune da ke yankin yammacin Jahar Maharashtra bayan shugaba Pranab Mukherjee ya yi watsi da koken Dan bindigar na neman Afuwa.
Wallafawa ranar:
Kasab ne kadai cikin ‘Yan bindigan da ya tsira da ransa, kuma kotu t ayi watsi da daukaka karar da ya yi a farkon watan nan, abinda ya sa aka kai shi gidan yarin Mumbai.
A shekarar 2010 ne aka yanke wa Kasab hukuncin Daurin rai da rai bayan kama shi da laifukan yaki da suka hada da kisa da ta’addanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu