Isa ga babban shafi
Kazakhstan

An yakewa shugaban ‘Yan adawar kasar Kazakhstan shekaru 7.5 a gidan yari

Wata kotu a kasar Kazakhstan ta yankewa shugaban ‘Yan adawar kasar daurin zaman gidan yari na tsawon shekaru 7.5 bayan an same shi da laifin tunzura yunkurin yin juyin mulki akan gwamnatin Shugaba Nursultan Nazarbayev.

Shugaban kasar Kazakhstan, Nursultan Nazarbayev
Shugaban kasar Kazakhstan, Nursultan Nazarbayev REUTERS
Talla

Kotun ta yankewa, Vladimir Kozlov, hukuncin ne bayan kuma an same shi da laifin hada wata haramtacciyar kungiya da kuma yin kira da a yi bore na tashin hankali akan gwamnatin kasar.

An dai kama, Kozlov ne a watan Janairu bayan wata zanga zanga da ma’aikatan Mai a kasar su ka gudanar wanda ya ayi sanadiyar mutuwar mutane 15.

Har ila yau za a kwace duk kayyakin Kozlov kamar yadda kotun ta ba da umurni.

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama dai sun yi Allah wadai da yadda ake muzgunawa Kozlov da kuma sauran kungiyon adawan kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.