Isa ga babban shafi
Japan

Masana kimiyyan Japan na kokarin magance matsalar rashin haihuwa

Kwararru a fannin kimiyar kasar Japan sun bayyana cewa, suna dab da samar da hanyar da zai magance matsalar rashin haihuwa a tsakanin Bil Adama, inda su ke kokarin kirkiro da kwayaye ta hanyar amfani da kwayoyin halittar matashin bera. Wannan cigaba zai bawa mata wadanda ke da matsalar haihuwa samar da kwayayen daga kwayoyin halittarsu wanda za dasa a jikinsu, a cewar masanan.  

Wasu masana kimiyyar kasar Japan
Wasu masana kimiyyar kasar Japan www.slashgear.com
Talla

“Wannan yunkuri idan har ya yiwu, zai taimaka mana wajen gano yadda ake samar da kwayaye a jikin Dan adam, wanda zai taimaka wajen gano meka hana wasu matan haihuwa.” Inji daya daga cikin masu binciken, Farfesa Michinori Saito.

Ya kara da cewa za kuma su cigaba da yin binciken akan Bil Adam da kuma Birrai, inda ya yi kasheda cewa ba wai an samar da hanyar magance matsalar haihuwa bane, domin akwai sauran jan aiki a gaba har yanzu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.